logo

HAUSA

Atiku Bagudu:Kasashen Sin da Najeriya za su kara hada karfin samun ci gabansu

2024-09-18 10:02:17 CMG Hausa

Daga ranar 4 zuwa ranar 6 ga watan Satumba, an gudanar da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC na shekara ta 2024 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabanni da manyan jami’ai daga kasashen Afirka fiye da 50 suka hadu a birnin Beijing.

A cikin shirinmu da ya gabata, mun ji ra’ayoyin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya Mohammed Idris, game da ci gaban dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Najeriya, da kuma wasu nasarorin da aka cimma karkashin dandalin FOCAC na wannan karo. A cikin shirin mu na yau, za mu gabatar muku da wata tattaunawa, tsakanin wakiliyar mu Fa’iza Muhammed Mustapha, da ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na Najeriya Atiku Bagudu.