Raya yankunan karkara domin manoma su kara jin dadin zamansu
2024-09-18 07:35:36 CGTN Hausa
A farkon makon jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin bunkasa masana’antu a matsayin jigon farfado da yankunan karkarar kasar Sin.
Shugaban na Sin, ya ce ya dace yankuna daban daban su bunkasa karfi da fifikon su, da bin tafarkin kara farfado da wurare gwargwadon yanayin su. Shugaba Xi ya yi kiran ne lokacin da yake ran gadi a birnin Tianshui, dake lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.
Yayin rangadin ya gana da manoman tufa, ya kuma ga irin fasahohin su na raya sana’a ta amfani da na’urorin zamani, da fasahohi masu inganci na noma da cinikayyar albarkatun gona. Har ma ya yi kira gare su da su yi amfani da zarafin da suke da shi na fadada sana’ar su don samun rayuwa mai inganci.
Yayin da Sin ke kara fadada ayyukan raya yankunan karkara ta fuskoki daban daban, fannin kiwon lafiyar al’umma na cikin sassan da ake baiwa muhimmanci. A baya bayan nan ma wasu rahotanni na cewa a bana gwamnatin kasar za ta tura tawagogin kiwon lafiya 44, zuwa yankunan tsakiya da na yammacin kasar mafiya koma baya a fannin kiwon lafiya, domin su samar da hidimomi ga masu bukata.
Yawan jami’an da za a tura yankunan karkara mafiya bukatar hidimomin kiwon lafiya a bana zai ninka na bara, kamar dai yadda hukumar lura da kiwon lafiya ta kasar ta sanar.
Tawagogin za su kunshi a kalla jami’ai 5, kuma za su yi aiki a larduna 17 ciki har da Xinjiang, da Xizang cikin a kalla makwanni 3.
Kuma bisa tsarin aikinsu, za a ba da fifiko ga yankunan da a baya ke cikin masu matsananciyar bukatar hidimar kiwon lafiya, da wadanda suke lunguna, da masu tarin kananan kabilu, ko wadanda ke da karancin ababen more rayuwa masu nasaba da kiwon lafiya.
Babban burin da ake fatan a cimma dai shi ne tabbatar da samar da hidimomin kiwon lafiya masu inganci ga al’ummun dake wadannan yankuna dake da koma bayan samun hakan.
A shekarar 2011, Sin ta samar da irin wadannan tawagogi 19 a karon farko wadanda suka yi aiki a lardunan kasar 18. Kuma ya zuwa shekarar 2023, yawan tawagogin jami’an kiwon lafiyar da suka gudanar da aiki karkashin wannan manufa ya kai 199, inda jami’ai 1,300 suka shiga wannan aiki.
Wadannan misalai ne kawai na yadda gwamnatin kasar Sin ke kara azamar warware matsalolin al’ummun karkara, da rage gibin dake akwai tsakanin ci gaban yankunan birane da na karkara. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)