logo

HAUSA

Sarkin Malaysia zai ziyarci kasar Sin

2024-09-18 20:36:30 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau Laraba cewa, bisa gayyatar da Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi masa, sarkin Malaysia Sultan Ibrahim Sultan Iskandar zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 19 zuwa ta 22 ga watan Satumba.

Ziyarar ta Sarki Sultan Ibrahim Sultan Iskandar ita ce ziyararsa ta farko a wata kasa da ba ta kungiyar ASEAN ba, tun bayan hawansa karagar mulki a matsayin shugaban kasa, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya bayyana a taron manema labarai da aka gudanar yau Laraba.   

Lin ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Malaysia, da daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta ci gaba da abokantakar gargajiya, da zurfafa alakarsu bisa manyan tsare-tsare, da fadada hadin gwiwar moriyar juna, da kara kyautata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Malaysia, da samun sabbin sakamako wajen gina al’ummar Sin da Malaysia mai makomar bai daya. (Yahaya)