Sin ta bukaci Isra’ila ta janye daga yankunan Palasdinu da ta mamaye
2024-09-18 10:15:20 CMG Hausa
Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta saurari kiran da kasa da kasa ke yi mata, na ta janye nan take daga yankunan Palasdinu da ta mamaye.
Da yake tsokaci yayin wani zama na musamman game da batun Palasdinu, Fu Cong ya bayyana cewa, kawo karshen mamayar na nufin shawo kan rashin adalcin da aka dade ana yi, kuma abu mafi muhimmanci shi ne, shimfida tubalin zaman lafiya.
Ya kuma jaddada cewa, kafa ‘yantattun kasashe biyu, ita ce kadai hanyar warware batun Palasdinu, kuma ita ce matsayar da kasashen duniya suka cimma.
A cewarsa, kasar Sin na kira da a kira babban taron kasashen duniya kan zaman lafiya, domin farfado da damarmaki a siyasance, na kafa kasashe biyu da kuma tsara jadawali da hanyar aiwatar da shi.
Ya kara da cewa, Palasdinu ta samu kujera tsakanin mambobin MDD, kuma ta gabatar da wani kuduri gaban zauren majalisar, wanda ke neman ya mayar da hankali wajen aiwatar da shawarar da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICJ) ta bayar.
Bugu da kari, wakilin na Sin ya ce kasarsa za ta kada kuri’ar amincewa da kudurin, kuma tana fatan kudurin zai samar da sabon kuzarin kawo karshen mamayar da kafa ‘yantattun kasashe biyu, da kuma daukaka tsarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. (Fa’iza Mustapha)