Jaridar New York Times: Sin ta mamaye ci gaban duniya na amfani da makamashi mai tsafta
2024-09-18 11:00:35 CMG Hausa
Wani sharhi da jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa, ya bayyana yadda kasar Sin ta kankane wani rahoto kan ci gaban da aka samu a duniya game da amfani da makamashi mai tsafta da aka fitar a baya bayan nan.
A cewar sharhin, daga shekarar 2019 zuwa 2023, kasar Sin ta rubanya adadin karfin tashoshinta na samar da makamashi mai tsafta har fiye da sau 8, yana cewa, idan babu kasar Sin, duniya ba ta rubanya wannan adadi ko sau daya ba.
A cewar wani kiyasin da aka yi kwanan nan, kasar Sin ce take da kusan 2/3n dukkan manyan tashoshin samar da makamashi daga hasken rana da karfin iska da aka gina a duniya a bana.
Haka kuma, kasar Sin na taimakawa sauran kasashe komawa ga amfani da makamashi mai tsafta. A shekarar 2022, kusan kaso 90 na kayayyakin sola da aka samar a duniya, kirar kasar Sin ne.
Kasar Sin ta dora makomarta kan sabbin fasahohin makamashi, inda ta sha gaban alkawuran da ta yi wa duniya game da saurin komawarta ga amfani da makamashi mai tsafta. (Fa’iza Mustapha)