Wakilin kasar Sin ya bukaci Amurka da ta matsawa Isra’ila ta dakatar da ayyukan soji a Gaza
2024-09-17 16:41:04 CMG Hausa
Wakilin kasar Sin a jiya Litinin ya bukaci kasar Amurka da ta nuna halin da ya dace, da yin amfani da gagarumin tasirin da take da shi a kan Isra’ila, da kuma daukar matakai na zahiri don matsawa Isra’ila da ta tsagaita bude wuta a Gaza ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda kudurorin MDD suka bukata, don baiwa al’ummar Falasdinu da suka dade suna fama da wahala damar yin rayuwa.
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun Falasdinu, inda ya ce, duk da kudurori hudu da kwamitin sulhun ya amince da su, da umarnin da kotun duniya ta ba da na daukar matakan wucin gadi, da gagarumin kokarin MDD da sauran hukumomin jin kai, al'amuran jin kai a zirin Gaza na ci gaba da tabarbarewa, kuma ba a daina keta dokokin kasa da kasa, musamman ma dokokin jin kai na kasa da kasa ba.
Geng ya kara da cewa, kamar yadda bincike ya nuna, da a ce Amurka ba ta zama kashin wuya ba, da tuni kwamitin sulhun ya amince da kudurin neman tsagaita bude wuta tun farkon barkewar rikicin, kuma da a ce Amurka ba ta baiwa bangare guda kariya ba, da ba a yi watsi da bijirewa kudurori da dama na kwamitin sulhun ba.
Geng ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin sulhun da ya kara daukar matakan da suka dace domin kashe wutar yaki, da dakile bala'in jin kai, da samar da zaman lafiya a yankin cikin gaggawa. (Yahaya)