logo

HAUSA

An kammala bikin baje kolin CIFTIS tare da nasarori masu tarin yawa

2024-09-17 16:58:32 CMG Hausa

A jiya Litinin ne aka kammala bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na Sin, wato CIFTIS na shekarar 2024 a nan birnin Beijing, inda aka samu sakamako kusan 1,000 a aikace, kuma sama da kashi 20 cikin kashi 100 da suka halarci bikin baje kolin a zahiri, kamfanoni ne na kasa da kasa, a cewar mashirya bikin baje kolin.

Sakamakon da aka samu a bikin baje kolin na CIFTIS na wannan shekara sun hada da hada-hadar zuba jari da cinikayya a fannonin gine-gine, kudi da hidimomin kasuwanci. An gudanar da tattaunawa da harkoki sama da 180 yayin bikin na kwanaki biyar, kana fiye da kamfanoni 2,000 sun hallara a filin gudanar da bikin baje kolin, yayin da wasu sama da 6,000 suka halarci bikin baje kolin ta kafar intanet. A bikin baje kolin na wannan shekara, an yi nune-nunen fasahohin zamani masu yawa, alal misali, mutum-mutumin inji mai tiyatar kasusuwa da ke dauke da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam mai zurfi na AI, da mafi kankantar na’urar bugun zuciya a duniya da dai sauransu, fasahohin zamanin da suka kunshi sassan kirkirarriyar basira wato AI, da kwanfutoci masu sarrafa manyan bayanai, da fasahohin metaverse da 6G.

Jami'in ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Wang Bo ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, bikin baje kolin na CIFTIS na bana ya samu sakamako masu tarin yawa, lamarin da ya nuna cikakkiyar aniyar kasar Sin ta sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci ta hanyar bude kofa ga kasashen waje. (Yahaya)