Shugaba Tinubu ya ziyarci birnin Maiduguri domin gabatar da jajensa bisa iftila’in da ya faru na ambaliyar ruwa
2024-09-17 16:32:40 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa wajen tallafawa al’ummomin da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri ta jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Shugaban ya tabbatar da hakan ne jiya Litinin 16 ga wata lokacin da ya ziyarci birnin domin ganewa idanun sa adadin barnar da ambaliyar ruwan ya haifar, inda ya bayyana annobar a matsayin abin da ya shafi kasa baki daya .
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya ziyarci sansanonin da aka samar domin mutanen da wannan bala’i ya shafa, ya bayyana damuwarsa mutuka bisa irin asarar rayuka da na kaddarori da aka yi sakamakon wannan ambaliya.
Ya jajantawa cuncurondon mutanen da ya tarar a sansanonin tare da alkawarin cewa gwamantin tarayya za ta kara bijiro da wasu hanyoyin kyautata rayuwar su, inda ya yaba da namijin kokarin ma’aikatar gona ta tarayyar da gwamantin jihar Borno da kuma sauran al’umma da kungiyoyin bayar da agaji bisa tallafin da suka baiwa mutanen da annobar ambaliyar ruwan ta shafa.
Haka kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci shehun Borno, inda shi ma ya jajanta masa kasancewar ambaliyar ruwan ta shafi wani bangaren na fadarsa.
“Wannan hali da aka shiga yana da nasaba da matsalolin muhalli da suka hada da sauyin yanayi wanda kuma ya zamar mana wajibi mu yi kokarin shawo kan su daya bayan daya, sannan kuma dole ne mu ilimintar da al’ummarmu a game da matakan kariya da kula da ingancin muhalli.”
Shugaban na tarayyar Najeriya ya yi addu’ar Allah ya kare afkuwar irin wannan bala’i a nan gaba a jihar da ma kasa baki daya.(Garba Abdullahi Bagwai)