Kasar Sin ta lashe Gasar Fasaha ta duniya karo na 47
2024-09-16 16:05:26 CMG Hausa
'Yan gasar kasar Sin sun kankane teburin lambobin yabo yayin Gasar Fasaha ta duniya ta WorldSkills karo na 47, bayan sun lashe lambobin zinare 36, a gasar da aka kammala jiya Asabar a birnin Lyon na Faransa.
Baya ga lambobin zinare, sun kuma samu na azurfa 9 da na tagulla 4 da kuma lambobin yabo 8 na mafi gwaninta.
Har ila yau, an ba Sinawa biyu mahalarta gasar ta hada fasahohin zamani da ayyukan kirkire- kirkire da masana’antu ta Industry 4.0, lambar yabo ta alfarma ta Albert Vidal, saboda samun maki mafi yawa.
Yayin rufe gasar, an mika tutar gasar ta WorldSkills ga birnin Shanghai na kasar Sin daga birnin Lyon, wanda ke nufin birnin Shanghai ne zai karbi bakuncin gasar karo na 48. (Fa’iza Msutapha)