logo

HAUSA

Kasar Sin na girmama cikakken ‘yancin Serbia

2024-09-16 20:13:00 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar na girmama cikakken ‘yancin kan kasar Serbia da ikon da take da shi kan yankunanta, kuma tana ganin ya kamata a kare tsaro da halaltattun hakkokin Serbiyawa dake yankin Kosovo.

Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka a yau Litinin, lokacin da aka nemi jin ra’ayin kasar Sin kan batun na Kosovo, inda ya kara da cewa, daukar mataki na kashin kai ba zai taimaka wajen maganace batun ba, kuma yana kawo tsaiko ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin. Ya ce, ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki su ci gaba da tattaunawa mai ma’ana da kuma lalubo mafita mai dorewa ga batun.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan sandan dake hukumomin wucin gadi na Pristina, sun kai samame tare da kwace iko da hukumomin dake kula da harkokin ‘yan asalin Serbia dake arewacin Kosovo. ‘Yan sandan Kosovo sun kuma tsare Serbiyawa 4 tare da kwace takardun kudin Serbia daga bankin kasa ta Serbia dake arewacin Kosovo. Ana sake fuskantar yanayin zaman dar dar a wannan yankin na Kosovo. Shugaban Serbia Aleksandar Vucic, ya mayar da martani da kausasan kalamai ta wani jawabi da ya yi da aka watsa ta gidan talabijin. (Fa’iza Mustapha)