Yara mata a karkarar Sin na kokarin sauya makomarsu ta hanyar buga kwallon kafa
2024-09-16 16:29:44 CMG Hausa
Makarantar firamare ta Zhangpan dake gundumar Mengjin na birnin Luoyang dake lardin Henan a tsakiyar kasar Sin, tana nan kamar dai kowacce makarantar kauye. Makarantar na da dalibai 271, kuma tana karantar da manhajar ilimin firamare. Sai dai, makarantar tana da wani abu na musammam. Cikin shekaru 7 da suka gabata, kungiyar kwallon kafa ta mata ta makarantar ta lashe gasannin a matakan gunduma da birni da lardi har da na kasa da kasa sau 15 gaba daya. Da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar makarantar, sun shiga kungiyoyin kwallon kafa na lardin ko na kasar Sin. Sabo da kaunarsu ga wasan kwallon kafa, musamman la’akari da horo mai tsanani da ake ba su, ‘yan matan na kauye, sun samu dimbin damammaki a rayuwarsu.
Bisa la’akari da kwazon wadannan yara mata ‘yan wasan kwallon kafa, ma’aikatar kula da ilimi ta ayyana makarantar firamare ta Zhangpan a matsayin ta matakin kasa mai manhajar wasan kwallon kafa. Song Haibo, shugaban makarantar ya bayyana cewa, “kwallon kafa ya koyar da daliban cewa, za a iya samun kalubale da rashin nasara a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, gano musabbabin rashin nasarar, tare da ci gaba da nuna kwazo.”
Watakila Song da ‘yan wasan ba za su taba mantawa da matakin karshe na gasar cin kofin gwamnan lardin Henan ba a shekarar 2019. ‘Yan wasan sun yi atisaye sosai domin gasar, kuma ba su gamu da wahalhalu sosai a gasar ba, yayin da suka doke dukkan abokan karawarsu domin zuwa matakin karshe. Song ya ce, “mun dauka cewa, tabbas za mu lashe gasar, har mun shirya liyafar murna. Sama da mutane 100 na kauyen Zhangpan ne suka je filin wasa domin ba ‘yan wasan kwarin gwiwa yayin wasa na karshe.” Sai dai an samu akasi. Ga mamakin kowa, kungiyar ta yi rashin nasara, lamarin da ya sa ‘yan wasan kuka.
Duk da wannan rashin nasara, an jinjinawa basira da kwazon ‘yan wasan. Daga cikin tsoffin ‘yan wasan kungiyar, Liang Jiaqi, ta shiga kungiyar wasan kwallon kafa ta lardin Fujian, yayin da Song Jiaqi wadda ita ce ‘yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle na matakin kasa, tare da Wang Yihao suka shiga kungiyar kwallon kafa ta lardin Jiangxi. Sauran mambobin kungiyar kuma sun shiga manyan makarantun sakandare na birnin Luoyang. Wang ta shiga kungiyar ne lokacin da take aji na 3. Mahaifinta Wang Huzhan, ya ce ya fi son ta koyi rawa maimakon kwallon kafa. Amma Wang Yihao ta nace ta fi son kwallon kafa. “Ko bayan ta kammala makarantar firamare, ta ci gaba da atisaye karkashin fitilun titi da dare,” cewar mahaifinta Wang Huzhan. Jajircewar ‘yarsa ya burge shi.
Ba da jimawa ba, Wang Yihao ta zama daya daga cikin muhimman ‘yan wasa. Wang Huzhan ya kan je kallon wasannin da take bugawa daga nesa da filin wasa ba tare da saninta ba.Ya ce, “ina tsoron kar ta dimauce idan ta gan ni.”
A bara, Yuan Jiaxin mai kaunar kwallon kafa, wadda take aji na 6, ta koma makarantar. Sai kuma ta shiga kungiyar, kuma nan da nan ta kara gogewa. Ta ce “ ina son zama kwararriyar ‘yar wasan kwallon kafa, kuma ina son in fafata a gasar cin kofin duniya a matsayin ‘yar wasan kungiyar kasar Sin.” Daga cikin ‘yan wasan da suka kammala karatu a makarantar Zhangpan shekaru 5 da suka gabata, an ayyana 5 a matsayin ‘yan wasa na kasa na ajin farko, yayin da aka ayyana 7 a matsayin ‘yan wasan kasa na aji na biyu.
Song Haibo ya furta cewa, “har yanzu, ba abu ne mai sauki ba da ‘yan matan kauye su sauya makomarsu.” Yanzu kungiyar makarantar na da ‘yan wasa 26 daga ajujuwa daban-daban, amma abu mai bacin rai shi ne, ba su isa ba ga masu bayar da horo idan suka so su zabi wadanda za su buga gasanni.
Liang Yaowu, mai aikin horo a makarantar ya kirkiro wani salon motsa jiki na kwallon kafa, wanda ke tattare da motsin da a kan yi akai-akai yayin kwallon kafa. A kullum, a lokacin hutu, dukkan daliban firamaren Zhangpan na motsa jiki, kowannensu tare da kwallo. Song ya ce, “Kwallon kafa hanya ce ta kaucewa kiba fiye da kima da kuma cutar damuwa. Yana kuma taimakawa yara fahimtar burikansu da ka’idoji da hadin kai.” Yanzu, kowanne dalibi na da damar bugawa ajinsa kwallo a kungiyar makarantar. Jami’an makarantar sun cimma yarjejeniya da wata makarantar horar da wasanni dake karkashin jami’ar Luoyang. Daliban da suke neman kwarewa a fagen kwallon kafa a makarantar, za su taimaka wajen horar da ‘yan makarantar firamare ta Zhangpan.
A watan Maris na shekarar 2024, hukumar kula da harkokin wasanni ta kasar Sin da wasu hukumomi 11, suka fitar da wasu ka’idojin gyare-gyare da raya wasannin kwallon kafa tsakanin matasan kasar Sin. Yayin wani rangadi, daga ranar 30 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu na shekarar 2024, mambar majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, ta ziyarci makarantu da sansanonin horar da kwallon kafa a lardin Hubei dake tsakiyar kasar da kuma lardin Jiangxi dake gabashin kasar. Yayin rangadin, ta ce ya kamata a yi kokarin kafa wani tsarin horar da kwallon kafa a wasu wurare na gwaji, musamman a yammacin kasar Sin, da zummar samar da karin masu basirar kwallon kafa. Ta kuma yi kira da a inganta tsarin gasar kwallon kafa tsakanin matasa.
Song Haibo ya bayyana cewa, “muna fatan kowanne yaro ya taso cikin koshin lafiya da annashuwa, kuma muna fatan wadanda ke kaunar kwallon kafa, za su samu karin damammaki domin samun ci gaba”. (Kande Gao)