logo

HAUSA

Guguwar Bebinca ta yi wa Shanghai tsinke

2024-09-16 16:39:21 CMG Hausa

Guguwar Bebinca, wato guguwa ta 13 da aka gani a bana, ta yi wa Shanghai tsinke da misalin karfe 7:30 na safiyar yau Litinin,

A cewar cibiyar kula da yanayi ta birnin Shanghai, guguwar tafiyar iskarta ta kai mita 42 kan kowacce dakika, ta fara ne daga yankin Lingang na gundumar Pudong.

An yi imanin cewa, Bebinca ita ce guguwa mafi karfi da birnin Shanghai ya fuskanta cikin shekaru 75, inda ta zo da iska mai matukar karfi da mamakon ruwan sama. Hotunan dake yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ta tuge bishiyoyi da yadda sandunan fitilun titi suka fadi. (Fa’iza Mustapha)