logo

HAUSA

Jawabin shugaba mai ci na gamayyar kasashen Sahel AES albarkacin cikon shekara guda da kafuwarta

2024-09-16 16:49:26 CMG Hausa

A ranar jiya 15 ga watan Satumban shekarar 2024, shugaban kasar Mali kuma shugaba mai ci na gamayyar kasashen yankin Sahel da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso, Kanal Assimi Goita ya gabatar da jawabin cikon shekara guda na AES, wanda kasashen uku suka watsa kai tsaye ta gidajen talibijin da rediyo.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan jawabi, ga rahoton da ya hada mana.

 

Shi dai wannan jawabi na shugaban gamayyar kasashen AES ya tabo batutuwa da dama masu muhimmancin gaske da suka hada da yaki da ta’addancin a cikin shiyyar, da kokarin kasashen uku wajen neman cin gashin kansu, da kuma yadda al’ummomin kasashen uku suka nuna juriya da kawo goyon baya ga shugabannin sojojin kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali, tare da jinjinawa takwarorinsa na Nijar birgadiye janar Abdoudrahamane Tiani da kaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso kan nacewarsu wajen nema makoma mai haske ga al’ummominsu.

Haka kuma cikin jawabinsa na shekara guda na AES, shugaban gamayyar din ya kawo albishir, inda ya bayyana cewa a cikin kwanaki masu zuwa, za’a fara aiki da sabon fasfo na zamani bisa burin kara kyautata takardun tafiye tafiye cikin kasashen gamayyar AES, domin saukaka shige da ficen al’ummomi da dukiyoyinsu a cikin duniya baki daya, shirye-shiryen al’adu da wasannin motsa jiki da na ilimantarwa na kan hanya domin karfafa hadin kan al’ummominmu da kuma shirin kafa wata kafar watsa labaru ta hadin gwiwa domin samun zarafin watsa labaru masu kyau da tsari, da fa’ida cikin kasashenmu uku, in ji kanal Assimi Goita.

Inda kuma, ya ce ya ku al’ummar gamayyar kasashen yankin Sahel, muna jaddada a yau niyyarmu na karfafa kowace rana huldar dangantakarmu na dunkulewa da zumunci tsakanin al’ummominmu da taimakon juna domin yankin Sahel ya zama wani yanki na zaman lafiya, da zaman jituwa da ci gaba mai dorewa.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.