Fursunoni 281 aka tabbatar sun tsere sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri
2024-09-16 16:52:45 CMG Hausa
Hukumar lura da gidajen gyaran hali a tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, fursunoni 281 ne suka bace bayan da jami’an hukumar tare da taimakon wasu hukumomin tsaro suka kammala kwashe fursunonin zuwa wani waje na daban bayan da ambaliyar ruwa ya shafi wurin da ake tsare da su.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar na kasa Alhaji Abubakar Umar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Abuja cikin wata sanarwa jiya Lahadi 15 ga wata, ko da ya ce tun a jiyan an samu nasarar kame 7 daga cikin wadannan fursunoni.
Daga tarayyar Najeriy wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kakakin hukumar gyaran halin ta tarayyar Najeriya ya ce yanzu haka hukumar tana da cikakken bayanin fursunonin da suka tsere, wanda suke adane a ma’ajiyar na’urar kwamfuta, wanda kuma ya kunshe hotunansu.
Ya ce ambaliyar ruwan da aka samu ya yi sanadin faduwar katangar gidan da ake tsare da fursunonin da kuma na gidan ma’aikatan hukumar dake birnin na Maiduguri, kuma an gano bacewar mutanen ne a lokacin da ake tsaka da aikin kwashe su.
Kakakin hukumar gyaran halin ta tarayyar Najeriya Abubakar Umar ya ce, a halin yanzu hadin gwiwar jami’an tsaro tare da na hukumar sun bazu wajen neman fursunonin da suka tsere.
Ya kuma tabbatarwa al’umma cewa wannan abu da ya faru na tserewar fursunonin ba zai taba shafar yanayin zaman lafiya a birnin na Maiduguri da kewaye ba.(Garba Abdullahi Bagwai)