logo

HAUSA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar musulmi murnar bikin zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta

2024-09-16 16:51:09 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar musulmin kasar murnar bikin Maulidi, ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW wanda ya yi daidai da hijira 12 ga wata rabiyul-Auwal.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya Lahadi 15 ga wata a birnin Abuja wadda take dauke da sa hannun mashawarci na musamman ga shugaban a kan harkokin yada labarai Mr. Bayo Onanuga, shugaba Tinubu ya bukaci musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen tunawa da kyawawan halayen fiyayyen halitta tare da amfani da su wajen gudanar da mu’amullar su ta yau da kullum.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce hakika amfani da koyarwa Annabi Muhammadu SAW ita ce hanyar kadai da za ta iya hada kan al’ummar kasa ba tare da nuna bambancin jinsi ko addini ba.

Ya ce a lokacin yana raye manzon Allah annabi Muhammadu SAW ya yi koyi da al’umma su rinka tausayin juna, rashin nuna son kai, juriya da kulla alaka mai kyau a tsakanin jama’a, a don haka ya zama wajibi ga duk wani musulmi ya yi kokarin yin kwaikwayo da wannan halayya tagari.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, sau tari al’umma na shiga cikin rudu ne a duk lokacin da suka kaucewa umarnin ubangiji, a don haka akwai mutukar bukatar kowa ya shiga taitayinsa bisa la’akari da halin da Najeriya ta shiga na matsalolin daban daban kama daga na tsaro da kuma na tattalin arziki, wanda yanzu haka gwamnati keta kokarin ganin ta daidaita su.(Garba Abdullahi Bagwai)