logo

HAUSA

Shugaban Zambia: Kudurorin hadin gwiwar Sin da Afirka da Sin ta gabatar za su bunkasa nasarar hadin kan sassan 2

2024-09-15 17:16:25 CMG Hausa

Shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ya ce, kudurorin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka 10 da Sin ta gabatar, za su bunkasa nasarar hadin kan sassan biyu. Kuma hakan ya shaida yadda Sin da kasashen Afirka ke aiki tare wajen bunkasa kansu.

Shugaba Hichilema ya ce, hadin gwiwar sassan ya shafi fannonin raya tattalin arziki, da cinikayya da zuba jari, da raya ilimi, da al’adu da zamantakewa, da kyautata jin dadin jama’a, da samar da isasshen abinci da makamashi.

Shugaban na Zambia, wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kafar watsa labarai ta kasar Sin, yayin taron dandalin FOCAC da ya gabata a kwanan baya, ya ce kasashen Afirka za su iya tallafawa duniya wajen sauya akala zuwa samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Tasirin wannan sauyi kuwa, na iya samar da ci gaban tattalin arziki maras gurbata muhalli, da cin gajiyar makamashi maras gurbata muhalli, wadanda ka iya samar da yanayin duniya mai inganci da dorewa.

Har ila yau, a kan wannan turba, za a iya samar da karin guraben ayyukan yi a kasashen nahiyar da ma kasar Sin, kuma ma’anar hakan za ta zarce moriyar Afirka da Sin kadai.   (Saminu Alhassan)