logo

HAUSA

Matsakaicin adadin fasinjoji dake bin titunan mota a biranen kasar Sin ya doshi miliyan 200 a duk rana

2024-09-15 17:29:22 CMG Hausa

Ya zuwa karshen shekarar 2023 da ta gabata, matsakaicin adadin ababen hawa masu dakon fasinjoji dake zirga-zirga a titunan biranen kasar Sin ya kai 682,000, ciki har da na ababen hawa kirar bas masu amfani da sabbin makamashi da yawansu ya wuce kaso 80 cikin jimillar ababen hawan. 

Yanzu haka biranen kasar Sin 54, sun riga sun bude hanyoyin jiragen kasa har na tsawon kilomita fiye da dubu 10. Yayin da yawan fasinjojin da suke zirga-zirga ta ababen hawa a biranen Sin a kowace rana ya kai kimanin miliyan 200.

Mataimakin ministan harkokin sufuri na kasar Sin Li Yang ne ya yi bayani kan kididdigar, a gun bikin fadakarwa don gane da ra’ayin amfani da ababen hawa wajen zirga-zirga na shekarar 2024, wanda ya gudana a birnin Changchun dake lardin Jilin na kasar Sin a jiya Asabar.

Li Yang ya bayyana cewa, sa kaimi ga yin amfani da ababen hawa wajen zirga-zirga, shi ne zabi mafi dacewa yayin da ake zamanintar da biranen kasar Sin. Ya ce ya kamata a yi amfani da ababen hawa da farko don kawo sauki ga zirga-zirga a birane. Kana a yi amfani da ababen hawa don samar da gudummawa ga kiyaye muhalli a birane. (Zainab Zhang)