logo

HAUSA

Jami’an kare gurbatar muhalli na gwamnatin tarayyar sun isa garin Maiduguri

2024-09-15 16:28:23 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar muhalli na tarayyar Najeriya Alhaji Balarabe Abbas ya sanar da tura ma’aikatan sashen lura da gurbatar muhalli zuwa garin Maiduguri domin su shawo kan kalubalen gurbatar yanayi da kuma na muhalli a birnin sakamakon annobar ambaliyar ruwa.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ranar juma’a 13 ga wata lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, inda ya ce ma’aikatan za su yi aiki ne tare da sauran hukumomi da kungiyoyi da suke da ruwa da tsaki wajen kare muhalli.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministan ya ce a duk lokaci irin wannan na ambaliyar ruwa, a kan samu matsaloli na gurbatar muhalli wanda kuma ka iya haifar da barkewar cuttuttuka da dama baya ga mutuwar tsirrai da itatuwa.

Ya ce ayarin jami’an ma’aikatar tasa za su hada kai da takwarorinsu na jihar Borno domin gudanar da wannan aiki, inda ya tabbatar da cewa sun iso jihar da dukkan kayayyakin aikin da ake bukata.

Alhaji Balarabe Abbas ya ci gaba da bayanin cewa, ya zama wajibi a gaggauta daukar dukkan matakan da suka dacewa wajen dakile munmunan tasirin da annobar za ta haifar, haka kuma ya jaddada kudurin ma’aikatar muhallin ta tarayya wajen taimakawa gwamnatin jihar Borno da tsari dorarre da zai kawo karshen matsalolin muhalli da jihar ke cin karo da su.

Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yaba mutuka bisa yunkurin ma’aikatar muhallin ta tarayya, sanan ya yi kiran da a samar da mafita ta din-din-din da za ta warware matsalolin da dama-damai a jihar da kuma kalubalen kwararowar hamada.

Gwamnan wanda ya bayyana damuwarsa bisa yadda giwaye ke lalata gonaki a wasu kananan hukumomin dake jihar, inda ya bukaci ministan da ya agaza wajen shawo kan wannan matsala. (Garba Abdullahi Bagwai)