An yi bikin “Rubutu a samaniya: Labari na a kasar Sin” na murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a Jamus
2024-09-15 21:09:55 CMG Hausa
An yi bikin “Rubutu a samaniya: Labari na a kasar Sin” na murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a birnin Berlin na kasar Jamus a jiya Asabar, bikin da babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin jakadancin Sin dake Jamus, da kuma cibiyar mu’amala da hadin gwiwar harsunan Sin da kasashen waje ta ma’aikatar ilmi ta kasar Sin suka dauki nauyin gudanarwa.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya yi jawabi ta kafar bidiyo yayin bikin, inda ya ce a gabar da ake cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kafar CMG ta kaddamar da aikin “Rubutu a samaniya: Labari na a kasar Sin” a sassan duniya, kuma abokai daga kasashe fiye da 60 sun mika rubutunsu game da labarinsu a kasar Sin, wanda ya zarce 1600 ga kafar CMG, masu kunshe da rubutu a harsuna daban daban, da wakiltar ra’ayoyi da al’adu iri iri na kasashe daban daban, da nuna kyakkyawan fatansu na samun zaman lafiya da jin dadin rayuwa, da kuma sada zumunta a tsakanin al’ummomin kasa da kasa.
An ce, za a gudanar da bukukuwan “Rubutu a samaniya: Labari na a kasar Sin” a kasashen Amurka, da Canada, da Rasha, da Australia, da Saudiyya, da Mexico, da Najeriya da sauransu. (Zainab Zhang)