logo

HAUSA

A kalla mutane 41 ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a jihar Zamfara dake arewacin Najeriya

2024-09-15 16:54:46 CMG Hausa

A kalla mutane 41 ne suka mutu yayin wani hadarin jirgin ruwa a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara a arewacin Najeriya.

Hadarin dai ya faru jiya asabar 14 ga wata yayin da jirgin ya dauko wasu manoma 53, rahotanni sun tabbatar da cewa masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutane 12 ciki har da direban jirgin yayin da ragowar kuma suka nutse a cikin kogi, inda ake ci gaba da laluben su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kamar dai yadda shugaban riko na karamar hukumar Gummi Alhaji Na’Allah Musa ya shaidawa manema labarai, ya ce tun kafin jirgin ya fara tafiya sai da aka gargadi direban jirgin cewa ya rage adadin fasinjansa, amma hakan ya gagara, a sabo da haka nauyin da jirgin ya yi ne ya haifar da nutsewarsa .

Har dai ya zuwa safiyar yau Lahadi masu aikin ceto na ci gaba da lalubo ragowar gawawwakin da suka nutse.

Alhaji Shehu Muhammad shi ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, ta wayar tarho ya tabbatar da cewa,

“Ana nan ana ta kokarin yadda za a yi a ceto sauran mutanen da suka nutse a cikin ruwa, ‘yan sanda na nan da ‘yan CPG da ‘yan banga da wasu mutanen gari na kwarai ana nan ana ta kokarin a ga yadda za a yi a ceto su, mutane da yawa suna son yin tafiya inda za su je kuma jirgi daya ne a bakin kogin sai aka loda masa mutanen da suka yi masa yawa, ga kaya ga mutane da yawa wadannan dalilan ne ya sa jirgin ya nutse saboda nauyi ya yi masa yawa.”(Garba Abdullahi Bagwai)