logo

HAUSA

Me kuka sani game da bikin tsakiyar yanayin kaka

2024-09-14 17:13:19 CRI

Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiransa bikin Zhongqiu, ma’ana wato bikin tsakiyar yanayin kaka. Kuma a wannan shekara, zai fado ne a Talata mai zuwa, wato ranar 17 ga wata. A wannan rana, wata ya kan cika, kuma ya fi haske, kuma a lokacin da jama’a ke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, shi ya sa Sinawa suke kuma daukar bikin a matsayin bikin haduwar iyali.

Shin mene ne asalin bikin, kuma wadanne al'adu ne ke tattare da shi? A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske. (Lubabatu)