An kai wa shugaban Comoros hari
2024-09-14 15:26:08 CGTN Hausa
Fadar shugaban kasar Comoros ta sanar a jiya Juma’a cewa, an kai wa shugaban kasar Azali Assoumani hari da wuka, lokacin da ya halarci wani bikin ta’aziyyar wani sarki a kasar, inda ya ji dan rauni.
Sanarwar ta ce, shugaba Azali ya riga ya koma gida, kuma an cafke maharin. (Amina Xu)