logo

HAUSA

Sin ta maida martani kan matakan karshe da Amurka ta sanar na kara buga haraji kan wasu hajojin kasar Sin bisa sashi na 301 na dokar haraji

2024-09-14 20:53:46 CMG Hausa

Ofishin wakilin Amurka kan harkokin kasuwanci ya fitar da sanarwa game da matakan karshe da za a dauka bisa sashi na 301 na wata dokar cinikayya ta kasar a jiya, inda ya sanar da kara buga harajin kwastam kan wasu hajojin kasar Sin, al’amarin da ya fuskanci matukar rashin jin dadi da adawa daga kasar Sin.

Hukumar kula da kasuwanci ta kasa da kasa wato WTO ta riga ta yanke hukuncin cewa, sashi na 301 na dokar ya saba wa ka’idojin WTO din. Amma ita Amurka ba ta gyara kuskurenta ba, har ma ta kara buga wa hajojin kasar Sin harajin kwastam. Matakan da Amurka ta dauka bisa sashi na 301 na dokar haraji, matakai ne na nuna bangaranci gami da ra’ayin bada kariya ga kasuwanci, wadanda suka haifar da mummunar illa ga tsarin kasuwanci na kasa da kasa da tsarin masana’antu da na samar da kayayyaki a duniya. Kana, irin wadannan matakai, sun kasa daidaita matsalar gibin cinikayya da rashin karfin takara na masana’antu da Amurka ke fuskanta, har ma sun kara farashin kayayyakin da Amurka ta shigar da su daga kasashen waje, kuma kamfanoni da masu sayayyar kasar, su ne za su dandana kuda.

Ya dace Amurka ta gyara kuskurenta ba tare da bata lokaci ba, ta soke harajin kwastam da ta kara buga wa hajojin kasar Sin. Ita kasar Sin kuma za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba, don kare muradun kamfanoninta. (Murtala Zhang)