logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga Amurka da ta daina ci gaba da rarraba kawuna

2024-09-14 17:09:16 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Geng Shuang, ya bayyana a wajen taron duba batun samar wa kasar Ukraine makamai na kwamitin sulhu na majalisar cewa, ana fatan Amurka za ta daina ci gaba da rarraba kawuna, da haifar da fito-na-fito tsakanin sassan kasa da kasa, a maimakon haka, ya kamata ta taka rawar a-zo-a-gani a fannin kawo karshen yake-yake da wanzar da zaman lafiya.

Jami’in ya ce, shigar makamai a kai a kai, zai kara tsananta halin da ake ciki, da janyo karin asarar rayuka da dukiyoyi, da haifar da mummunar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya da ma shiyya-shiyya. A watan Mayun shekarar da muke ciki, kasashen Sin da Brazil sun fitar da wasu ra’ayoyi shida da suka cimma, wadanda suka shafi shawo kan rikicin kasar Ukraine ta hanyar siyasa, kana, kasashen Afirka sun bullo da manufofi guda goma don magnace rikicin Rasha da Ukraine. Al’amuran sun nuna cewa, yin shawarwari ta hanyar diflomasiyya da siyasa, ya dace da babban fatan akasarin kasashe da kuma daukacin al’ummu. Kasar Sin na fatan Amurka za ta saurari muryoyin kasa da kasa na neman samun zaman lafiya, da daina shafa bakin fenti ko kawo tsaiko ga kokarin diflomasiyya da kasar Sin da sauran kasashen duniya suke yi. (Murtala Zhang)