WHO ta amince da riga kafin cutar kyandar biri na farko
2024-09-14 17:01:36 CMG Hausa
Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta sanar da amincewa da riga kafin MVA-BN da kamfanin Bavarian Nordi A/S ya samar, a matsayin riga kafin cutar kyandar biri na farko da za a sanya cikin jerin riga kafin da hukumar ta amince da ingancinsu.
Darakta janar na hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wannan riga kafin cutar kyandar biri na farko da WHO ta amince da ingancinsa, muhimmin mataki ne a yakin da ake yi da cutar, ga yanayin barkewarta yanzu haka a nahiyar Afrika da ma nan gaba.
Ya nanata bukatar kara saye da rarraba riga kafin, domin tabbatar da adalci wajen samar da shi ga mafiya fuskantar barazana.
Ana bayar da riga kafin ne sau biyu da tazarar makonni 4 a tsakani, ga baligai masu shekara 18 zuwa sama. (Fa’iza Mustapha)