logo

HAUSA

Hukumar NEDC ta bayar da tallafin kayan abinci da na kwanciya ga mutanen da suka gamu da annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri

2024-09-14 10:57:52 CMG Hausa

Hukumar raya shiyyar arewa maso gabashin Najeriya NEDC ta bayar da tallafin kayayyaki ga wadanda suka gamu da annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno.

A lokacin da yake mika gudummawar kayan jiya Juma’a, manajan daraktan hukumar Mohammed Goni Alkali ya ce, kayayyakin sun kunshi na abinci da na sauran bukatun yau da kullum, kuma an samar da su ne domin rage kaifin asarar da mutanen suka yi sanadiyar wannan ambaliya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Nau’ikan kayayyakin dai sun kunshi buhuna dubu 10 na shinkafa da kantan dubu 10 na taliya, tabarmi dubu 15 da mayafai guda dubu 15.

Sauran sun hada da bukitai dubu 10 da katan dubu 5 na man girki da kunshin kayan yara dubu 5 da kuma rigunan sauro guda 7,500, inda kuma ya tabbatar da cewa, an damka kayan ga gwamnatin jihar Borno domin rabar da su.

Haka kuma Alhaji Muhammed Goni Alkali ya ce, hukumar ta kuma rabar da buhuna guda dari 2 na shinkafa da katan dubu 150 na taliya da katan dubu 250 na man girki da barguna guda dubu 200 da tabarmi guda dubu dari 2 da kananan kayan yara dubu guda 65 da kuma rigunan sauro guda dubu 20 ga jihohi shida dake shiyyar.

Shugaban hukumar ya ce, wannan tallafi na gajeren zango ne, inda ya ce, hukumar tana da tsarin raya shiyyar na dogo da matsakaicin zango. (Garba Abdullahi Bagwai)