logo

HAUSA

Sakon da aka isar game da yanayin tekun kudancin kasar Sin daga wasu taruka uku

2024-09-14 22:07:33 CMG Hausa

Daga CMG Hausa

Daga ranar 11 zuwa ta 13 ga wata, an gudanar da wasu taruka uku daya bayan daya, wato taron ganawa tsakanin jami’an kasashen Sin da Philippines kan batun tekun kudancin Sin, da taron dandalin tattaunawa kan batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 11 da aka gudanar a Beijing, sai kuma taron manyan jami’ai tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN dangane da yadda aka tabbatar da sanarwar bangarori masu ruwa da tsaki game da tekun kudancin kasar Sin(DOC). Tarukan ba batun tekun kudancin kasar kawai suka shafa ba, har ma da isar da sako na bai daya, wato a daidaita takaddama ta hanyar yin shawarwari da kiyaye kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, wanda shi ne burin bai daya na yankin.

Sinawa al’umma ce da ke rungumar zaman lafiya, sai dai hakan ba ya nufin za ta yi rangwame a kan ikonta a tekun kudancin kasar, wanda abu ne da kasar Philippines da ma wadda ke mara mata baya, ya kamata su fahimta. A yanayin da ake ciki na fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, aiwatar da shawarar kiyaye tsaron duniya da tabbatar da zaman lafiya da zumunta da hadin gwiwa a tekun kudancin kasar Sin, buri ne na bai daya na kasashen shiyyar. Kasar Sin za ta ci gaba da kokarin neman cimma wannan buri, kuma ya dace kasar Philippines ita ma ta gyara kuskurenta, ta rungumi daidaiton da kasashen yankin suka cimma, kuma ta yi zabin da ya dace da moriyarta. (Lubabatu Lei)