Kasar Sin ta bibiyi jiragen ruwan sojin Jamus da suka ratsa Zirin Taiwan
2024-09-14 16:15:54 CMG Hausa
Rundunar sojin ’yantar da jama’ar Sin ta yankin gabashi, ta ce ta bibiya tare da sa ido kan wasu jiragen ruwa 2 na sojin Jamus da suka ratsa Zirin Taiwan.
Kakakin rundunar mai mukamin babban Keftin Li Xi ne ya bayyana haka a yau Asabar, inda ya ce wucewar jiragen biyu da suka hada da jirgin yaki na “Baden-Württemberg” da na samar da kayayyaki na “Frankfurt am Main”, ta kara barazanar tsaro tare da aikewa da mummunan sako, yana mai cewa, har kullum, dakarun kasar Sin za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, domin dakile duk wani nau’i na barazana da takala.
A tsokacinta kan batun, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce ka’idar hadin gwiwar Sin da kasa da kasa, kuma ita ce matsayar da kasashen duniya suka cimma.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana hakan a jiya, inda ta ce kasar Sin na girmama ’yancin sufurin ruwa da dukkan kasashe ke mora a tekuna masu ruwa da tsaki, karkashin dokokin Sin da na kasa da kasa, ciki har da dokar MDD kan teku, amma kuma Sin din na adawa da fakewa da wannan ’yanci wajen yin takala da barazana ga cikakken ’yancin da ikonta kan yankunanta. (Fa’iza Mustapha)