Kasar Sin ta yi tir da zargin da aka yi wa ’yan wasan linkaya na kasar
2024-09-14 16:44:04 CMG Hausa
Hukumar yaki da amfani da ababen kara kuzari ta kasar Sin (CHINADA), ta soki takwararta ta Amurka (USADA) da jaridar New York Times, bisa zargi mara tushe da suka yi wa ’yan wasan linkaya na kasar Sin. Hukumar ta kuma soki Amurka bisa shiga batun da bata da hurumi, tare da kira da a yi wa ’yan wasan linkaya na Amurkar gwaji biyo bayan sauyi da launin fuskokinsu ya yi yayin gasar Olympics ta Paris.
Hukumar CHINADA ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a, bayan wani lauya mai zaman kansa mai suna Eric Cottier, ya gabatar da rahoto na karshe dake wanke ’yan wasan linkaya 23 na kasar Sin daga aikata laifi, ga kwamitin zartarwa na hukumar yaki da amfani da ababen kara kuzari ta duniya (WADA).
A cewar sanarwar, rahoton ya sake nuna dacewar bincike da matakin hukumar CHINADA ta dauka kan batun, tare da tabbatar da cewa babu wani batu na rufa-rufa kamar yadda wasu kungiyoyi da kafafen yada labarai irin su hukumar USADA da jaridar New York Times da ma kafar yada labarai ta Jamus, ARD suka yi ikirari.
CHINADA ta kuma zargi USADA da siyasantar da batun tare da sukarta bisa amfani da ta yi da dokar hana amfani da ababen kara kuzari ta Rodchenkov. Hukumar ta kuma yi kira da a yi wa ’yan wasan linkaya na Amurka gwaji, biyo bayan batun sauyin launin fuskarsu yayin gasar Olympics ta Paris. (Fa’iza Mustapha)