logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a hada karfi don tabbatar da zaman lafiya yayin da ake fuskantar sauye sauye

2024-09-13 21:01:57 CMG Hausa

Ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya yi kira ga kasashe su hada karfi wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin da ake fuskantar sauye-sauye a duniya. 

Cikin jawabinsa yayin bude taron tsaro na 11 na Xiangshan na Beijing, Dong Jun ya yi kira ga kasa da kasa su girmama juna da hulda da juna cikin sahihanci tare da samar da yanayi mai kyau na mu’amala da juna ta hanyar hakuri da sabanin dake akwai tsakaninsu.

Ya ce ya kamata kasa da kasa su tsare gaskiya su yi hadin gwiwar moriyar juna ta yadda dukkan bangarori za su amfana, da hada hannu domin cimma zaman jituwa mai dorewa cikin zaman lafiya.

A cewarsa, rundunonin sojin kasar Sin ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, kuma a shirye suke su samar da wani sabon tsarin hadin gwiwar tsaro da rundunonin soji dake fadin duniya.

Taron na bana mai taken “Inganta Tsaro Domin Makoma ta Bai Daya,” ya samu baki mahalarta sama da 1,800 daga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 100. (Fa’iza Mustapha)