logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya halarci dandalin masana’antu da kasuwanci na Sin da UAE

2024-09-13 11:01:48 CGTN Hausa

 

Da yammacin jiya Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci dandalin masana’antu da kasuwanci na Sin da hadaddiyar daular Larabawa ko UAE, wanda ya gudana a Dubai, inda kuma ya gabatar da jawabi.

Cikin jawabin nasa, Li ya nuna cewa, a halin yanzu, huldar Sin da hadaddiyyar daular Lararaba wato UAE na kan wata mahada mai muhimmanci, dake hade lokutan da suka gabata da ma nan gaba, kuma wani zarafi ne na karfafa ingantacciyar hadin gwiwarsu a bangaren raya tattalin arziki da cinikayya.

Kaza lika ya yi fatan kamfanonin kasashen biyu za su yi amfani da kyawawan damammaki wajen raya hadin gwiwar kut da kut tsakanin kasahen biyu. Da ma amfani da sabon zarafi na raya shawarar “ziri daya da hanya daya” mai inganci. Kana da gaggauta shigar da su cikin tsarin samar da hajoji a duniya, ta hanyar kara hadin gwiwarsu a bangaren habaka kasuwanni, da kara mu’ammala da tuntubar juna, da samar da manyan ababen more rayuwa, da tattara jari da sauransu, bisa muradun kasashen biyu da hangen nesa kan halin da ake ciki a duniya.

Wakilai kimanin 200 daga gwamnatoci, da kungiyoyin kasuwanci, da kamfanoni na kasashen biyu ne suka halarci taron. Kuma wakilan masana’antu da kasuwancin na UAE sun jinjinawa kuzari, da boyayyen karfi da kasuwannin Sin ke nunawa, suna masu sa ran kara zuba jari a Sin bisa shawarar, da ma kara hadin gwiwarsu ta fuskar samar da manyan ababen more rayuwa, da kimiyya da fasahohin kirkire-kirkire, da albarkatun makamashi da sauransu. (Amina Xu)