Daliban kasar Nijar 13 za su yi karatu a kasar Sin
2024-09-13 09:16:02 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, hukumomin kasar ne suke ci gaba da karfafa dangantakarsu ta fuskar man fetur tare da kasar Sin. Hakan kuma tare daliban kasar Nijar 13 da suka samu kudin karatu a kasar Sin tare da taimakon kamfanin Wapco.
Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Ministan man fetur, dokta Sahabi Oumarou ne ya jagoranci a ranar 12 ga watan Satumban shekarar 2024 a birnin Yamai da bikin tafiyar wadannan dalibai ’yan Nijar goma sha uku da suka amfana da kudin karatu a kasar Sin.
Wannan shiri yana cikin tsari ganuwa da hanya da kamfanin da ke kula da harkokin man fetur na kasar Sin WAPCO ya shirya da kuma zuba kudi tare da hadin gwiwar ma’aikatar man fetur ta kasar Nijar da kuma ma’aikatar ilimi mai zurfi, da binciken kimiyya da kirkire-kirkire.
Wannan kuma na nunawa tare da bayyana niyyar kasar Nijar na kara karfafa huldar dangantaka da kuma yaukaka kwarewarta a bangaren man fetur tare da taimakon kyakkyawar dangantaka tare da kasar Sin, in ji dokta Sahabi Oumarou, ministan man fetur din Nijar a gaban mambobin gwamnatin Nijar, da wakilan kamfanin WAPCO dake Nijar.
Su dai wadannan dalibai goma sha uku za su kwashe tsawon karatunsu a fannin man fetur, domin kasancewa nan da ’yan shekaru masu zuwa, kwararru bisa aikin da ya jibanci man fetur da makamantansa, haka kuma ta yadda kasar Nijar za ta ci gajiyar arzikin man fetur dinta daga dukkan fannoni.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.