Xi Jinping ya mika sakon taya murnar budewar dandalin Xiangshan na Beijing karo na 11
2024-09-13 11:04:33 CGTN Hausa
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar budewar dandalin Xiangshan na Beijing karo na 11.
A cikin sakonsa, Xi ya ce, Sin za ta ci gaba da tabbatar da shawarar tsaron duniya da gaggauta mabambantan bangarori da su kai ga matsaya daya don kawar da tushen dake haifar da rikice-rikicen duniya da kyautata tsarin tsaron duniya, ta yadda za a iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya cikin dogon lokaci, duba da cewa, ana fuskantar sanye-sauyen da ba a taba ganin irinsa a karni da ma al’ummomin duniya na matukar bukatar tsaro. Yana mai fatan a taka karin rawa wajen tinkarar kalubalolin tsaro a duniya cikin hadin gwiwa da gaggauta aikin kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya bisa ka’idar daidaito da bude kofa da yin hakuri da juna da koyi da juna da kai ga matsaya daya da zurfafa amincewa da juna. (Amina Xu)