Shugaban kasar Rasha ya gana da Wang Yi
2024-09-13 11:10:41 CMG Hausa
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke ziyarar aiki a Rasha. Yayin ganawar da ta gudana jiya Alhamis a birnin St. Petersburg, shugaba Putin ya ce kasarsa a shirye take ta karfafa daidaito tare da Sin ta fuskar manufofin samar da ci gaba, tare da ingiza alakar Rasha da Sin zuwa wani sabon matsayi.
A nasa tsokacin, Wang, wanda shi ma ya kasance mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin, cewa ya yi Sin na da kwarin gwiwa game da amincewa juna, da kawancen dake tsakanin sassan biyu.
Game da batun taron kungiyar BRICS dake tafe cikin wata mai zuwa a birnin Kazan na kasar Rasha kuwa, Wang ya shaidawa shugaba Putin cewa Sin za ta baiwa Rasha dukkanin goyon baya, kana za ta yi aiki tare da daukacin kasashe mambobin BRICS, wajen baiwa kungiyar damar ba da gudummawa ga gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.
Kaza lika, Wang ya jaddada kudurin kasar Sin na goyon bayan warware rikicin Ukraine ta hanyar sulhu. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da dukkanin sassan da batun ya shafa, wajen tattaro muryoyi na adalci da sanin ya kamata daga daukacin sassan kasa da kasa don cimma wannan buri.
Rahotanni daga ma’aikatar harkokin wajen Sin, sun nuna cewa shugaban na Rasha da mista Wang, sun yi muasayar ra’ayoyi game da batun kasar Ukraine, kuma shugaba Putin ya jaddada matsayar Rasha ta ci gaba da bude kofar tattaunawa, tare da jinjinawa matsaya 6 da kasashen Sin da Brazil suka cimma a watan Mayun da ya gabata, don gane da matakan warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Saminu Alhassan)