Hukumar NEMA tare da hadin gwiwa da rundunar soji na ci gaba da aikin ceto a birnin Maiduguri
2024-09-13 09:14:58 CMG Hausa
Hukumar bayar da agajin gaggawa a tarayyar Najeriya, wato NEMA tare da hadin gwiwa da rundunar sojin kasar da kuma sauran kungiyoyi sun matsa kaimi wajen gudanar da aikin ceto ga sauran al’umomin da suka rage a gidajen da ambaliyar ruwa ya cinye a wasu sassa na birnin Maiduguri.
Mukaddashin babban jami’in shiyyar arewa maso gabashi na hukumar NEMA Sirajo Garba ne ya tabbatar da hakan jiya Alhamis, 12 ga wata a Maiduguri yayin wata ganawa da manema labarai. Ya ce, mutane da dama ne har ya zuwa jiya Alhamis suke a makale a gidaje inda suke dakon masu aikin ceto.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Jami’in hukumar ta NEMA ya ce, hukumar ta samar da manyan motoci da jiragen ruwa inda suke aiki tare da sojoji wajen aikin ceton al’umma musamman ma a yankunan Abba-ganaram da Muna da rukunin gidajen 505.
Ya ce, a halin da ake ciki ma’aikatan hukumar ta NEMA sun sami nasarar ceto mutane kusan dari 2 a tsakanin ranar Laraba da kuma jiya Alhamis, amma kamar yadda ya fada a ranar da annobar ta auku an sami ceto mutane 1,000 yayin da kuma aka tsugunar da sama da mutane dubu 70 a wasu sansanoni guda 7 da aka samar.
A game da adadin mutanen da suka mutu kuwa, Alhaji Sirajo Garba ya ce, ba za a iya tantancewa yanzu ba sai na gaba kadan kasancewar yanzu ruwan ya fara janyewa.
Ha’ila yau kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulrahman Abdulrazak sun kai ziyarar jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Borno, inda a yayin ziyarar, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayar da gudumawar naira miliyan 50 a matsayin tallafi ga wadanda wannan annoba ta shafa. (Garba Abdullahi Bagwai)