logo

HAUSA

Mali: Hukumar OCLEI na karfafa kariyar masu bankado labari domin yaki da cin hanci

2024-09-13 11:06:37 CMG Hausa

A kasar Mali, babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa OCLEI ta kasa ta dauki nagartattun matakai a ranar jiya 12 ga watan Satumban shekarar 2024 a cibiyarta dake birnin Bamako domin bada kariya ga masu bankado labari, muhimman masu ruwa da tsaki wajen yaki da cin hanci.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Su dai wadannan nagartattun matakan karfafa kariya sun hada musamman ma da kin bayyana sunan mai bankado labari ta yanar gizo ko ta wata kafa ta daban, da neman gida a unguwar dake tsaro ko kuma wani wuri na daban, da ba su damar sakaya sunansu ko boyayyen suna domin kare kansu da kuma dauka ko nadar bayanai cikin kariya.

A cewar hukumar OCLEI, daukar wadannan matakai na da manufar ba da kwarin gwiwa da ba da yarda domin ’yan kasar Mali su ci gaba wajen bayyana mutane da suka salwanta dukiyar kasa da yin allawadai da ayyukan cin hanci da rashawa, ta yadda ’yan kasa za su kawo tasu gudunmawa wajen rage asarar kudade masu yawa da gwamnatin kasar Mali take fuskanta.

Ba da kariya ga masu bankado labari kan mutanen da suka yi wa tattalin arziki zagon kasa, wani muhimmin mataki ne domin bunkasa adalci cikin harkokin tafiyar da arzikin kasa da kuma mulki na-gari a kasar Mali.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.