A shirye kasar Sin take ta fadada cinikayya da Hadaddiyar Daular Larabawa
2024-09-12 21:04:19 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, a shirye Sin take ta fadada yawan cinikayyar dake tsakaninta da Hadaddiyar Daular Larabawa, da hada gwiwa a bangaren makamashi mai tsafta da motoci masu amfani da lantarki da kere-keren kayayyaki masu inganci da bangaren ilimin halittu da kiwon lafiya da tattalin arziki na dijital da hada hannu wajen tsara makomar masana’antu masu tasowa da ma wadanda za su bullo a nan gaba, tare da samun karin sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
Li Qiang ya bayyana hake ne yayin ganawarsa da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
A cewar firaministan na Sin, a shirye kasarsa take ta ci gaba da hada hannu da Hadaddiyar Daular Larabawa da sauran mambobin kungiyar hadin kan yankin Gulf (GCC) domin gaggauta kammala tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci tsakanin Sin da kungiyar ta GCC.
A nasa bangare, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya ce Haddadiyar Daular Larabawa, ta amince da manufar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta zama abokiyar hulda da za a iya dogaro da ita ga kasar Sin, haka kuma muhimmiyar abokiyar hulda a hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai inganci. (Fa’iza Mustapha)