Shugaba Xi ya yi kira da a samar da sabbin nasarori wajen kare muhallin halittu a Rawayen Kogi
2024-09-12 20:48:52 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a samar da sabbin nasarori wajen kare muhallin halittu tare da ci gaba mai inganci a Rawayen Kogi.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli mai kula da aikin soji ta kasar, ya bayyana haka ne a yau, yayin wani taro da ya kira a Lanzhou, babban birnin lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)