logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta yi gargadin cewa za a iya samun karuwar masu kamuwa da zazzabin Lassa a kasar

2024-09-12 10:15:07 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gargadin cewa akwai alamu dake nuna za a samun karuwar mutane da za su kamu da cutar zazzabin Lassa a kasar.

Darakta janaral na hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa Dr. Jide Idris ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba 11 ga wata a birnin Abuja yayin wani taron manema labarai. Ya ce ya zama wajibi a ankarar da al’umma saboda a takaita yawan masu kamuwa da ita wadda ta kan shafi kusan dukkan jihohin kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Dr Jide idris ya ce, ko da yake an dan sami raguwar cuttuttuka da dama a kasar, amma dai cutar zazzabin Lassa na cikin cututtukan da su kan bulla a duk shekara wanda kuma ana gab da shiga lokacin.

Ya ce, bisa la’akari da yadda yanayi ke sauyawa, hukumar ta yi hasashen samun karuwar bullar cutar cikin watanni kadan masu zuwa, wannan ce ta sanyawa ma yanzu haka hukumar ta himmatu wajen shirye-shiryenta domin dai ganin ta rage mummunar tasirin da ake kyautata zaton cutar za ta iya yi ga lafiyar al’umma.

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka a tarayyar Najeriya ya ce, a halin yanzu an sami rahoton alamun cutar ta Lassa har 7,973 inda daga cikin wannan adadin an tabbatar da mutane 982 sun kamu da ita yayin da kuma mutum 168 suka mutu. (Garba Abdullahi Bagwai)