logo

HAUSA

Babban sakataren cibiyar ACBF ya yi maraba da aniyar kasar Sin ta tallafawa noma da shawo kan kalubalen sauyin yanayi

2024-09-12 10:15:56 CMG Hausa

Babban sakataren asusun bunkasa sanin makamar aiki na Afirka ko ACBF, mista Mamadou Biteye, ya yi maraba da aniyar kasar Sin ta tallafawa sha’anin noma, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi a nahiyar Afirka.

Sakataren na ACBF, cibiyar dake aiki karkashin kungiyar AU, wadda kuma ke da matsuguni a birnin Hararen kasar Zimbabwe, ya yi tsokacin ne yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, yana mai cewa kasashen Afirka za su ci gajiya mai tarin yawa daga ilimi, da kirkire-kirkire, da gogewar kwararrun kasar Sin a fannin raya noma.

Yayin taron FOCAC na 2024 da aka kammala a makon jiya, kasar Sin ta alkawarta fadada hadin gwiwa da kasashen nahiyar Afirka, tare da aiwatar da manufofin hadin gwiwa 10 cikin shekaru 3 masu zuwa.

A fannin raya noma kuwa, Sin ta yi alkawarin taimakawa kasashen nahiyar da dabaru daban daban, ciki har da gina cibiyoyin baje fasahohin noma na zamani, da tura kwararrun masanan noma na Sin zuwa kasashen Afirka, da kafa kawancen raya noma ta amfani da kimiyya da fasaha na Sin da kasashen Afirka.

A cewar Biteye, matakin kasar Sin na tallafawa kasashen Afirka, a fannin gina ababen more rayuwa, musamman masu nasaba da dakile sauyin yanayi, da masu jure tasirinsa, muhimmin jigo ne ga cimma burin nahiyar na zamanantar da kai, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi.(Saminu Alhassan)