A shirye Sin take ta tsara yarjeniyoyin ciniki cikin ’yanci da karin kasashe masu tasowa
2024-09-12 20:36:17 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce har kullum, kasar kan nace ga adawa da kariyar cinikayya, tare da nacewa ga inganta ci gaban duniya ta hanyar cinikayya da rage gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kasashe. Kuma a shirye take ta tsara yarjeniyoyin ciniki cikin ’yanci da karin kasashe masu tasowa.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Alhamis.
Rahoton yanayin cinikayya a duniya na shekarar 2024 da hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) ta fitar a baya bayan nan, ya jaddada muhimmancin cinikayya wajen rage talauci da samar da ci gaba na bai daya, tare da bayyana cewa, tsananta kariyar cinikayya ka iya mayar da hannun agogo baya, ta fuskar rage gibin dake tsakanin masu hannu da shuni da masu karamin karfi, da shekaru 30. A cewar darakta janar ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala, karuwa da kyautatuwar harkokin cinikayya ka iya ba karin mutane da yankunan damar dunkulewa zuwa karfin tattalin arzikin duniya
A cewar Mao Ning, kasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudunmuwa ga aiwatar da harkokin cinikayya cikin ’yanci. Ta ce yayin taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, shugaban Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarwarin hadin gwiwa 10, ciki har da hadin gwiwa domin inganta ci gaban cinikayya tare da sanar da fadada bude kofar kasuwar kasarsa da soke haraji kan wasu kayayyaki da suka cancanci biyan kaso 100 bisa 100 na haraji, wadanda suka fito daga kasashen Afrika mafiya rangwamen karfi, inda kasar Sin ta zama babbar kasa mai tasowa ta farko, kuma mai karfin tattalin arziki a duniya, da ta aiwatar da wannan shiri. (Fa’iza Mustapha)