logo

HAUSA

An dakatar da shirye-shiryen TV5 MONDE a tsawon watanni 3 bisa dalilin rashin girmama ka’idodin aikin jarida

2024-09-12 09:59:59 CMG Hausa

A jamhuriyyar kasar Mali, hukumomin kasar ne suka dauki matakin dakatar da watsa shirye shiryen kafar TV5 Monde domin maida martani kan wani rahoton da gidan talabijin din na kasar Faransa ya watsa dake batun yaki da ta’addanci na rundundar sojojin kasar Mali mai iyaka da kasar Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A cikin wata sanarwa ce ta hanyar gidan rediyo da talabijin na kasar Mali da aka fitar a ranar jiya, babbar hukumar daidaita harkokin sadarwa cewa HAC ta bayyana janye tashoshin gidan talabijin din kasar Faransa TV5 Monde har tsawon watanni uku, wannan kuma tun daga ranar Laraba 11 ga watan Satumban shekarar 2024. Shi dai, wannan mataki ya biyo bayan take wasu ka’idodin aikin jarida da suka bayyana karara a cikin wani rahoton da tashar kasar ta Faransa ta watsa a ranar 26 ga watan Augustan shekarar 2024.

Wannan rahoton da ake magana kansa ya shafi batun yakin da kasar Mali take yi da ta’addanci, da ake ganin an yi amfani da son kai da rashin adalci wajen tsara wannan rahoto. Dan jaridar da ake zargi, ya gabatar illa da ra’ayin bangare guda ba tare da jin bangaren gudan ba. Haka kuma ba tare da ra’ayin rundunar sojojin kasar Mali ba a hukumance, da yin amfani da zato wajen bada labari ba tare da tabbatar da sahihancinsa ba.

Wannan dakatarwa ta biyo bayan wani kashedi na farko na babbar hukumar daidaita harkokin sadarwa ta kasar Mali ta yi wa gidan talabijin na TV5 Monde a cikin watan Mayun shekarar 2023 duk dai bisa dalilai iri guda.

A cewar babbar hukumar HAC, wannan hukunci an aiwatar da shi bisa la’akari da dokoki da kundin sadarwa da ke aiki a kasar Mali.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.