logo

HAUSA

Wang Yi ya yi kira ga kasashe masu tasowa su hada hannu wajen inganta tsaro da ci gaba a duniya

2024-09-12 20:03:27 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin kuma daraktan ofishin hukumar koli kan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya yi kira ga kasashe masu tasowa da su hada hannu wajen bayar da gudunmuwa ga gina duniya mai zaman lafiya da tsaro na bai daya.

Wang Yi, wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne yayin wani taron tattaunawa tsakanin manyan jami’an dake da hakkin kula da tsaro ko bayar da shawarwari kan tsaro daga kasashen BRICS da kasashe masu tasowa, a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

A cewarsa, a matsayinta na mamba cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta kan tsaya tsayin daka tare da kasashe masu tasowa da hada hannu da su, wajen tabbatar da adalci da inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.

Ya ce Sin na maraba da karin kasashe masu tasowa dake da ra’ayi daya da ita, su shiga cikin kungiyar BRICS da hada hannu domin zama wani karfi mai ingiza zaman lafiya da kwaniciyar hankali, kuma kashin bayan ci gaba da jagorantar harkokin duniya da koyi da juna tsakanin mabambantan al’ummu, ta yadda za a kai ga gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil’adama. (Fa’iza Mustapha)