logo

HAUSA

Wang Yi ya yi kira ga kasashe mambobin BRICS da su yi hadin gwiwar shawo kan kalubalen tsaro

2024-09-12 10:45:18 CMG Hausa

Darakta a ofishin hukumar koli mai lura da harkokin waje a kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Wang Yi, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar BRICS, da su yi hadin gwiwa wajen shawo kan kalubalen tsaro.

Wang Yi ya yi kiran ne yayin wani taron manyan jami’ai da ya gudana a jiya Laraba, a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha, inda ya ce a wannan gaba da ake fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban daban, kamata ya yi kungiyar BRICS ta samar da wata mahanga ta dogon lokaci, kana ta kara aiwatar da matakai a bude, da hada karfi da karfe tare, don shawo kan kalubalen tsaro da magance matsaloli masu nasaba da hakan, ta yadda za a ingiza sabon karfi na magance yanayin tangal tangal a matakin kasa da kasa, da samar da sabuwar gudummawa ta gina dauwamammen zaman duniya da tsaron kasa da kasa.

Domin cimma wannan buri a cewar mista Wang, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda 4, wadanda suka hada da bukatar aiwatar da matakan samar da zaman lafiya. Da gina tsarin tabbatar da tasirin sassa daban daban. Da yayata warware batutuwa ta hanyar siyasa. Da kuma kare adalci da daidaito.

Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe mambobin BRICS, wajen aiwatar da cikakken shirin wanzar da tsaron kasa da kasa, da ci gaba da zurfafa hadin gwiwar BRICS ta fuskar siyasa da tsaro, da gina duniya mai zaman lafiya da daidaito, da hada hannu wajen rungumar kyakkyawar makoma tare.  (Saminu Alhassan)