logo

HAUSA

Li Qiang ya gana da yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya

2024-09-12 12:48:48 CGTN Hausa

 

Da yammacin jiya Laraba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya tattauna da yarima mai jira gado na masarautar Saudiyya, kana firaministan gwamnatin kasar Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, tare da jagorantar taron kwamitin hadin kai na manyan jami’an Sin da Saudiyya karo na 4 cikin hadin gwiwa.

Li ya ce, huldar kasashen biyu na samun bunkasuwa cikin sauri a dukkanin fannoni masu zurfi, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, har ma an kai ga samun ci gaba mai armashi a mabambantan bangarori. Ya ce Sin na daukar huldar kasashen biyu da muhimmanci a harkokin diflomasiyyarta, musamman ma a yankin Gabas ta Tsakiya. Kana tana fatan ci gaba da goyon juna baya, da taimakawa juna, da ma mai da bunkasuwarsu zuwa matsayin dammamaki masu kyau, ta yadda za a gaggauta ci gaban huldar kasashen biyu, da kara amfanar da al’ummun kasashen biyu.

A nasa bangare, yarima mai jira gado Muhammad bin Salman, cewa ya yi kasashen biyu na daukar matsayi iri daya a harkokin kasa da kasa, suna sauke nauyin dake wuyansu cikin hadin gwiwa. Ban da wannan kuma, suna nacewa ga mutunta ikon mulki na sauran kasashe, da nuna adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe.

Har ila yau, Saudiyya na jinjinawa matsayi na adalci da Sin take dauka kan batun Palasdinu, kuma Saudiyya na fatan kara hadin gwiwa da Sin a harkokin kasa da kasa, da ma taka rawar gani wajen kiyaye zaman lafiya, da tsaro da kwanciyar hankali a duniya.  (Amina Xu)