Nijeriya Ta Samu Lambobin Yabo 7 A Wasannin Nakasassu Ta Bana
2024-09-12 16:28:59 CRI
Nijeriya ta kammala gasar wasannin nakasassu ta shekarar 2024 a birnin Paris da samun lambobin yabo bakwai da suka hada da zinare biyu, da azurfa uku, da tagulla biyu, inda ta zo ta 40 cikin kasashe 83.
‘Yar wasan Nijeriya mai suna Folashade Oluwafemiayo ce, ta jagoranci nasarorin, inda ta samu lambar zinare tare da karya tarihin duniya guda biyu a bangaren mata masu daga nauyin kilo 86.
Ta zama ‘yar wasa ta farko da ta samu wannan nasara, inda ta tabbatar da matsayinta na zakarar Paralympic sau biyu.
ta ma Onyinyechi Mark ta dauki zinari a Para-powerlifting, yayin da Flora Ugwunwa, Esther Nworgu, da Bose Omolayo, wadanda suka samu azurfa a bangaren Para-powerlifting mai nauyin kilogiram 79, sun bayar da gudunmawar lambobin yabo da bajintar da suka nuna.
Eniola Bolaji ta kafa tarihi bayan ta samu kyautar tagulla a wasan badminton.
An kammala wasannin ne a filin wasa na Stade de France, inda kasar Sin ke kan gaba a teburin gasar bayan da ta karya tarihin duniya da kyaututtuka 29.
Yadda Sabon Tsarin Kofin Zakarun Turai Zai Kasance
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid mai rike da kofin gasar zakarun Turai ta Champions za ta fafata da Liberpool a zagayen farko na gasar da aka sauya wa fasali ta 2024-25 a sabon tsarin da hukumar ta nahiyar turai ta fitar.
A satin da ya gabata ne aka raba jadawalin sabon tsarin gasar da za a fara amfani da shi a kakar wasa ta bana mai kungiyoyi 36 kuma sauran kungiyoyin da Real Madrid za ta fafata da su a zagayen su ne Dortmund, AC Milan, Atalanta, Salzburg, Lille, Stuttgart, Brest.
Muhimmin sauyi da kwamitin zartarwa na UEFA ya sanar shi ne ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi a baya, inda a yanzu kowace kungiya za ta buga wasa takwas – hudu a gida, hudu a waje, amma ba gida da waje ba.
Talla
A baya matakin rukuni na gasar zakarun Turai ya kunshi kungiyoyi 32, da ake rabawa cikin rukuni takwas, inda kowanne rukuni ke kunshe da kungiyoyi hudu, sannan sauran wasannin da za su fi zafi a zageyn sun hada da wanda PSG za ta kara da kungiyoyin Manchester City, Bayern Munich, Atletico Madrid, Arsenal.
Yadda jadawalin sabon tsarin zai kasance
A yanzu kungiyoyi 36 ne za su shiga gasar, mai tsarin lig daya, inda duka kungiyoyin za su kasance a teburi daya domin tantance kungiyoyin da za su fafata da juna, da farko an rarraba su a cikin tukwane hudu bisa matsayin kowace kungiya.
An yi amfani da wata manhaja da UEFA ta samar domin fitar da kungiyoyin da kowacce kungiya za ta fafata da su kuma a matakin farko babu kungiyar da za ta fafata da abokiyar hamayyarta da suka fito daga kasa daya. Hakan na nufin kowace kungiya za ta kara da kungiyoyi biyu daga kowace tukunya cikin hudu.