logo

HAUSA

Karfin tattalin arzikin masana’antun Sin na karuwa sosai

2024-09-11 11:38:35 CGTN Hausa

 

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton bayani kan ci gaban bunkasuwar tattalin arziki da al’umma a cikin shekaru 75 da suka gabata tun daga kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949. A cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, tattalin arzikin masana’antun Sin na samun ingantacciyar bunkasuwa, inda kasaitacciyar bunkasuwarta ta karu matuka.

Daga ciki, darajar masana’antun Sin ta karu da kashi 10.5% a kowace shekara daga shekarar 1952 zuwa 2023, wanda aka kimanta bisa farashin da bai canja ba. Bankin Duniya ya ba da alkaluma cewa, a karon farko yawan karuwar masana’antun samar da hahoji na Sin ya zarce Amurka tun daga shekarar 2010, wanda ya kai matsayin koli a duniya, kuma ya kai kashi 30.2% bisa na yawan duniya a shekarar 2022, lamarin da ya bayyana cewa, Sin ta zama muhimmin jigo ga bunkasuwar tattalin arzikin masana’antun duk duniya baki daya.

A shekarar 2023, yawan hajojin lantarkin da Sin ta fitar zuwa ketare ya kai kashi 58.5% na dukkan hajojin da ta fitar, daga cikinsu yawan motoci ya kai miliyan 5.22, lamarin da ya sa Sin ta zama kasa ta farko a duniya wajen fitar da motoci zuwa ketare. (Amina Xu)