Sin ta ba da shawarar a yi amfani da makamashin nukiliya lami lafiya don amfanawa al’lummar kasashe masu tasowa
2024-09-11 14:30:24 CGTN Hausa
Jiya Talata, wakilin dindindin na kasar Sin dake IAEA jakada Li Song ya halarci taron majalisar kungiyar ta watan Satumba, inda ya yi jawabi kan kimiyya da fasahar nukiliya da yadda Sin ta yi amfani da su, kuma ya jadadda shawarar da Sin take bayarwa na yin kira da a yi amfani da makamashin nukiliya lami lafiya don amfanawa al’ummar kasashe masu tasowa.
Li ya ce, hadin gwiwar makamashi da kimiyyar nukiliya za ta zama wata muhimmiyar hanya ta kara mu’ammala da tuntubar Sin da Afirka da ma kawo amfani ga kasashen Afirka har ma kasashe masu tasowa baki daya. Sin ta yi kira ga IAEA da ta yi la’akari da bukatun wadannan kasashe masu tasowa da daukar matakan da suke dacewa, da ma daukar hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare da amfanawa kasashe masu tasowa da muhimmanci, ta yadda za ta daga karfin mambobinta a bangren amfani da kimiyyar nukiliya. (Amina Xu)