Jami’i: Kasar Sin Babban Tushen Jarin Kasashen Waje Ga Kasar Zimbabwe
2024-09-11 11:42:49 CMG Hausa
Jami’in gwamnatin Zimbabwe ya bayyana a jiya Talata cewa, ana samun karuwar zuba jari a kasar, inda kasar Sin ke ba da gudummawa sosai ga shigowa jarin kasashen waje cikin kasar.
Mataimakin babban sakataren ofishin shugaban kasa da majalisar ministocinsa William Manungo ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake amsa tambayar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi a gefen taron masu ruwa da tsaki na hukumar zuba jari da raya kasar Zimbabwe ko ZIDA a takaice, da aka gudanar a birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe, inda ya ce, har yanzu kasar Sin ta kasance muhimmiyar abokiyar zuba jari ta kasar Zimbabwe, musamman a fannin hakar ma'adinai da masana'antu.
Ya kara da cewa, jarin da kasar Sin ta zuba ya ta'allaka ne kan hakar ma'adinai, amma baya ga zuba jari a fannin hakar ma'adinai, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Zimbabwe da jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta samar da jari mai tsoka a fannin sufuri, da makamashi da dai sauransu.
Rahoton na ZIDA na shekarar 2023 ya nuna cewa, an bai wa masu zuba jari na kasar Sin lasisi 369 kuma an yi hasashen darajar jarin da suka zuba ya kai dalar Amurka biliyan 3.93, wanda ya kai kusan kashi 40 cikin dari na darajar da aka yi hasashe na shekarar. (Yahaya)