Kashim Shettima: Ambaliyar ruwa ta Maiduguri annoba ce mafi tsanani a tsawon shekaru 30
2024-09-11 09:13:12 CMG Hausa
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bayyana annobar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri a matsayin mafi tsananin annoba da aka taba fuskanta a tsawon shekaru 30 da suka gabata.
Ya tabbatar da hakan ne jiya Talata 10 ga wata yayin da ya ziyarci wuraren da annobar ta fi kamari a birnin domin kimanta adadin asarar da aka tafka.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Sanata Kashim Shettima ya ce, duk da dai cewa asarar da annobar ta haifar ya wuce a iya kimanta ta, amma dai gwamnatin tarayya za ta bayar da kulawar da ta kamata wajen kyautata rayuwar al’umomin da suka gamu da wannan iftila’i.
“Mun zo wannan waje ne bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin dai mu jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa faruwar wannan annoba.”
Sanata Kashim Shettima ya ce, hakika wannan annoba tamkar dai tana tunatar da mu ne ci gaba da karuwar barazanar sauyin yanayi a duniya baki daya ba kawai ga shiyyar arewa masu gabashin Najeriya ba.
Ya kara jaddada cewa, gwamnati za ta kara himmatuwa sosai wajen bullo da tsare-tsare ingantattu da za su yi maganin faruwar irin wannan mummunar annoba a nan gaba a jihar da ma sauran sassan kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)